Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Sin ta aiwatar da matakai a bude tare da nuna sanin ya kamata yayin da take yaki da COVID-19
2020-05-18 20:03:09        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce tun da fari, kasarsa ta rika aiwatar da matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a bude, ba tare da wata rufa-rufa ba, ta kuma yi aiki tare da nuna sanin ya kamata.

Xi wanda ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, cikin jawabin da ya gabatar ta kafar yanar gizo, yayin taro na 73 na wakilan dandalin kula da lafiya na daniya karkashin hukumar WHO, ya ce Sin ta gabatar da bayanai ga WHO, da sauran kasashen da batun ya shafa a kan lokaci. Kaza lika kasar ta gabatar da yanayin kwayar cutar cikin sauri.

Shugaba Xi ya ce "Mun gabatar da bayanai game da dabarun shawo kan ta, da na magani da muka samu kwarewa a kan su, ga sauran sassan duniya ba tare da wata rufa-rufa ba. Mun yi dukkanin abun da za mu iya don tallafawa, da taimakawa kasashen dake da bukata.

A wani ci gaban kuma, shugaban na Sin, ya ce kasar sa na shirin kafa wani tsarin hadin gwiwa na asibitocin Sin da takwarorin su dake kasashen Afirka sama da 30. Har ila yau Sin za ta gaggauta gina helkwatar cibiyar dakile cututtuka ta CDC a nahiyar, a wani mataki na samar da ikon kintsawa barkewar cututtuka, da shawo kan su a dukkanin sassan nahiyar ta Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China