Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin da Habasha da sauran kasashen Afirka za su ci gaba da yaki da COVID-19
2020-05-12 11:33:11        cri
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya ce kasar sa a shirye take, ta yi hadin gwiwa da 'yan uwanta na Afirka, ciki hadda kasar Habasha, ta yadda za a kai ga cimma nasarar shawo kan cutar numfashi ta COVID-19 a daukacin nahiyar Afirka.

Wang Yi, wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa ta wayar tarho da takwaran aikin sa na Habasha Gedu Andargachew a jiya Litinin, ya kuma ce tun bullar wannan annoba, Habasha ke nuna cikakken goyon bayan ta ga kasar Sin. Yayin da kuma wannan cuta ke kara yaduwa a sassan Afirka, jami'in ya ce Sin ta samar da taimako sau da dama ga nahiyar, a wani mataki na tallafawa ga kawar da cuta baki daya.

Wang, ya kuma ce kawancen Sin da Afirka ya jure kalubale mai tarin yawa, a fage na cudanyar kasa da kasa, kuma manufofin kasar Sin na wanzar da abota tare Afirka ba su taba canzawa ba. Daga nan sai ya jaddada bukatar goyon bayan juna, da nuna fahimtar juna tsakanin sassan biyu, musamman a wannan lokaci da ake tsaka da yaki da cutar COVID-19.

A daya bangaren kuma, Wang Yi ya soki wasu kasashen duniya dake nuna yatsa ga Sin, bayan kuwa irin wadannan kasashe sun gaza, wajen aiwatar da matakan yaki da wannan annoba a cikin gida, yana mai cewa, yunkurin su na shafawa Sin bakin fenti zai fuskanci kalubale daga kasashen duniya, ciki hadda nahiyar Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China