Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba a samu sabon mai kamuwa da cutar COVID-19 a cikin gidan Sin ba
2020-05-12 11:08:13        cri
Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Talata cewa ba a samu sabon rahoton mai kamuwa da cutar COVID-19 a cikin gidan kasar ba a ranar Litinin.

Sai dai an samu rahoton mutum guda da ya shigo da cutar daga ketare a yankin Mongolia ta gida mai cin gashin kai, kamar yadda hukumar lafiyar ta tabbatar da hakan cikin bayyanan da ta saba fitarwa a kowace rana.

Sannan kuma a ranar Litinin din, a samu sabon rahoton mutum guda wanda ya shiga da cutar daga kasar waje a birnin Shanghai.

A cewar hukumar lafiyar, babu rahoton mutuwa mai alaka da annobar COVID-19 a wannan rana ta Litinin.

Bugu da kari a ranar litinin din, an sallami mutane 27 daga asibiti bayan sun warke daga cutar, yayin da adadin mutanen dake cikin tsakanin fama da cutar ya karu da mutum guda zuwa mutane 10.

Ya zuwa ranar Litinin, baki dayan adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da annobar COVID-19 a dukkan yankunan kasar Sin ya tasamma 82,919, cikinsu har da mutane 115 da suke cigaba da samun kulawar likitoci, yayin da mutane 78,171 tuni aka sallamesu daga asibiti bayan sun warke daga cutar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China