Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasikar Xi Jinping ga daliban Pakistan dake kasar Sin
2020-05-18 14:46:40        cri

Jiya Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta wata wasika ga daliban Pakistan da suke karatu a jami'ar fasaha da kimiyya ta Beijing, inda ya yiwa wadannan fitattun matasa maraba da zuwa nan kasar Sin, kuma ya karfafa musu gwiwar kara yin mu'ammala da hadin kai da matasan kasar Sin da na kasa da kasa ta yadda za su sa kaimi ga kara tuntubar juna tsakanin jama'ar kasa da kasa da ba da gudunmawar raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya.

A cikin wasikar da Xi Jinping ya rubuta, ya ce, bayan barkewar cutar COVID-19, gwamnatin kasar Sin da makarantu na mai da hankali sosai kan tsaro da kuma lafiyar daliban ketare dake kasar, tare da ba su taimako a duk fannoni. Kana daliban suna karawa Sinawa kwarin gwiwa ta hanyoyi daban-daban yayin da Sinawa ke kokarin yakar cutar, abin da ya shaida dankon zumunci tsakaninsu.

Yanzu haka akwai daliban Pakistan 52 dake karatu a jami'ar fasaha da kimiyya ta Beijing. Kwanan baya, sun rubuta wa shugaba Xi Jinping wasika don nuna godiya kan taimakon da jami'ar ta ba su bayan barkewar cutar, da bayyana aniyyarsu ta ba da gudunmawarsu wajen aiwatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya"da inganta zumuncin dake tsakanin Sin da Pakistan bayan sun kammala karatunsu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China