Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin: Yukurin tsoma batun Taiwan cikin abubuwan da aka tattauna a babban taron hukumar WHO ba zai samu goyon baya daga al'ummar duniya ba
2020-05-19 20:40:37        cri
Game da shawarar da wasu kasashe suka gabatar, ta gayyato yankin Taiwan, don ya halarci taron hukumar lafiya ta duniya WHO a matsayin mai sa ido, shugaban babban zauren hukumar WHO karo na 73, ya ce ba za a tattauna batun ba a yayin taron wannan karo.

Don gane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Talata cewa, wannan ya sake shaida cewa, yunkurin neman balle yankin Taiwan daga kasar Sin ba zai yi nasara ba. Kana yadda ake neman tsoma batun Taiwan cikin abubuwan da aka tattauna a babban taron hukumar WHO, ba zai samu goyo baya daga al'ummun duniya ba.

Zhao ya ce, mambobin hukumar WHO suna tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da bin wasu kudirorin da babban zauren MDD, da na hukumar WHO suka zartas, da kokarin tabbatar da adalci a harkokin duniya, don haka kasar Sin na matukar jinjina musu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China