2020-05-12 20:05:58 cri |
Kalaman nasa na zuwa ne, bayan da sashen kula da harkokin waje na hukumomin yankin na Taiwan ya sanar a jiya Litinin cewa, a shekarar 2005, babban yankin kasar Sin ya sanya hannu kan wata takardar fahimtar juna ta sirri (MOU) da WHO kan harkokin da suka shafi shigar yankin na Taiwan ayyukan da suka shafi WHO.
Zhao ya jaddada cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma yankin Taiwan wani bangare na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba. Yana mai cewa, kasar Sin ba ta bukatar sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da duk wata hukumar kasa da kasa na dawo da yankin bangaren kasar Sin.
Ya ce, daga shekarar 2019 zuwa wannan lokaci, rukunoni 16 cikin 24 na masana lafiya daga Taiwan sun shiga ayyukan WHO. Yana mai cewa, yadda mahukuntan yankin Taiwan suke sanya siyasa wajen jirkita batun annobar COVID-19, shirme ne kawai. (Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China