Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shawarci mahukuntan jam'iyyar DPP ta yankin Taiwan su daina yaudarar kansu
2020-01-23 20:28:02        cri
A kwanakin baya ne, kawancen wasu jam'iyyun siyasa uku na kasar Sao Tome and Principe ya fitar da wata sanarwa, inda ya ce, rahoton da aka ruwaito na cewa, wai daya daga cikin membobinsa, kana tsohon shugaban kasar, Fradique Bandeira Melo de Menezes ya taya Tsai Ing-wen murnar zama jagorar yankin Taiwan, ba shi da gaskiya ko kadan. Game da haka, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasarsa tana shawartar mahukuntan jam'iyyar DPP ta Taiwan da su daina yaudarar kansu, don kar duniya ta yi musu dariya.

Geng ya ce, manufar kasar Sin daya tak a duniya, wata muhimmiyar ka'ida ce ta alakar kasa da kasa kuma batu ne da kasashen duniya suka iya na'am da shi. Tun lokaci da Sin da Sao Tome and Principe suka dawo da huldar diflomasiyya a tsakaninsu sama da shekaru uku, alaka tsakanin sassan biyu ta bunkasa yadda ya kamata, kuma sakamakon wannan alaka a fannoni da dama sun amfani al'ummomin kasashen biyu.

Duk wani yunkuri ko yaudara na gurgunta dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Sao Tome and Principe ba zai yi nasara ba.(Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China