Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na adawa da matakin Amurka na zartar da dokar dake da alaka da Taiwan
2020-03-28 16:51:26        cri
Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ta bayyana adawa da rashin jin dadinta kan matakin Amurka na zartar da dokar kare dangantakar Taiwan da kawayenta ta 2019.

Sanarwar da kwamitin kula da harkokin wajen kasar na majalisar ya fitar, ta ce an zartar da dokar duk da adawa mai karfi da Sin ta nuna.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Geng Shuang, ya bayyana a jiya cewa, Sin na bukatar Amurka ta gyara kuskurenta, kada ta awaitar da dokar, kuma kada ta kawo tsaiko ga yunkurin wasu kasashe na hulda da kasar Sin, ko kuma Sin din ta mayar da martanin da ya dace. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China