Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkawarin da Xi Jinping ya yi ya bayyana yadda kasar Sin take kokarin sauke nauyin dake bisa wuyan wata babbar kasa
2020-05-19 18:14:31        cri

An kaddamar da babban taron majalisar kiwon kafiya ta duniya WHO na shekara-shekara karo na 73, a jiya Litinin ta kafar bidiyo a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Taron na bana, ya zo a daidai lokacin da duniya ke fuskantar kalubalen lafiya da ba a taba ganin irinsa ba. Cikin mahalarta taron, har da Shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda aka yi masa gayyatar da ya bayar da wani jawabi a yayin bikin kaddamar da taron, inda ya ce abu ne mai matukar muhimmanci a gudanar da taron a wannan lokaci da ake fuskantar annobar COVID-19 da ta kasance kalubale mafi tsanani tun bayan yakin duniya na 2, wadda kuma ta yi sanadin rayuka sama da dubu 300 a fadin duniya.

Sanin kowa ne cewa, annobar ta shafi tattalin arzikin kowacce kasa da ma duniya baki daya, inda a karon farko cikin shekaru da dama tattalin arzikin kasar Sin ya fuskanci koma baya. Sai dai duk da wannan kalubale da ake fuskanta, a cikin jawabin nasa, shugaba Xi Jinping ya yi alkwarin cewa kasarsa za ta bada gudunmmawar dala biliyan 2 cikin shekaru 2 domin tunkarar tasirin annobar COVID-19. Wannan mataki ya nuna matsayin kasar Sin na babbar kasar da ba al'ummarta kadai ta sa a gaba ba, har ma da sauran al'ummar duniya.

Baya ga haka, ya ce kasar Sin za ta kafa wani tsarin hadin gwiwa, ta yadda asibitocinta za su hada gwiwa da asibitoci 30 na Afrika da gaggauta ginin hedkwatar cibiyar yaki da cututtuka da kandagarkinsu ta nahiyar. Wannan ya shaida irin aminci da karamci da dangantaka mai karfi dake tsakanin Sin da Afrika. Bisa la'akari da yadda tsarin kiwon lafiya a nahiyar ke da rangwamen inganci, wannan yunkuri na kasar Sin, zai taimaka wajen karawa nahiyar karfin tunkarar annoba da kula da lafiyar al'ummarta. Har ila yau, zai taimaka wajen kara gogayya tsakanin masanan harkokin lafiya na bangarorin biyu, tare da kara fahimta tsakanin al'ummomin kasashen, wanda ake fatan ya dore har zuwa zuri'a ta gaba, ta yadda za a ci gaba da dorar da zumuncin dake tsakanin al'ummun kasashen, wanda kuma ya kasance daya daga cikin burika da manufofin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC).

Ban da haka, Shugaban ya ce dole ne a kara taimakawa nahiyar Afrika a yakin da take da cutar. Inda ya ce kasar Sin a bangarenta, ta aike da tallafi da kayayyakin kiwon lafiya masu tarin yawa ga sama da kasashen Afrika 50 da kuma Tarayyar Afrika. Ta kuma tura tawagogi 5 na jami'an kiwon lafiya zuwa nahiyar. Inda yanzu haka, ake da tawagogi 46 na jami'an lafiya na kasar da suke taimakawa kokarin dakile cutar COVID-19 a nahiyar.

Har ila yau cikin jawabin, ya tabu batun hada hannu da kungiyar G20 wajen jinkirtawa ko dakatar da biyan bashi ga kasashe mafi fama da talauci. Wato duba da mummunan tasirin cutar COVID-19, za a dagawa kasashe masu fama da talauci kafa wajen biyan basussukan da ake binsu. Irin wannan mataki shi kasar Sin ta dauka a cikin gida, wanda ya kara taimaka mata a fannin farfado da ayyukan da ceto kananan da matsakaitan kasuwanci da kamfanoni daga durkushewa. Ga shi kuma, za ta taimaka wajen aiwatar da wannan shiri a kan kasashen waje masu rangwamen kudin shiga. Irin wannan lamari, shi ke nuna cewa kasar Sin ba ta daukar ci gaban wasu kasashe a matsayin barazana, wannan ya nuna tare da bayyana ra'ayin gina al'umma mai makoma iri guda ga dukkan bil adama.

Hakika kasar Sin ta cancanci yabo da jinjinawa, domin a duk inda aka tabo al'amuran da suka shafi duniya, to sai ta tabo batun tallafawa kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afrika. Har kullum ta kan yi kokarin jan hankalin sauran kasashe da su tallafawa kasashen Afrika tare da sanya batutuwan da suka shafe su a kan gaba.

Yayin da wasu kasashen duniya suka fi mayar da hankali kan batutuwan cikin gida da siyasa da raya kansu da neman shafawa wasu bakin fenti, kasar Sin ta dukufa wajen shawo kan cutar a cikin gida, a daya bangaren kuma, tana kokarin ganin ta taimakawa kasashe da yankunan da ba su kai ta karfi ba, ba tare da la'akari da matsalolin da take ciki ba. Wannan akida ta kasar Sin ta sa jami'ai da dama na Afrika sun kiranta da abokiyar arziki da za a iya dogaro da ita a koda yaushe, cikin matsala ko kalubale. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China