Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Duk da kalubalolin da duniya ke fuskanta na annobar COVID-19 kamfanonin aika sakonni na Sin sun samu bunkasuwa
2020-05-18 19:17:46        cri

Bayan shafe sama da watanni hudu ana fama da matsalar yaki da annobar cutar numfashin ta COVID-19 a sassan duniya daban daban, inda kawo yanzu annobar ta yi sanadiyyar rayukan sama da mutane dubu dari 200 a fadin duniya kana sama da mutane miliyan 4 sun kamu da cutar a fadin duniya, kawo yanzu, kasar Sin ta samu manyan nasarari wajen yaki da cutar ta COVID-19, koma za'a iya cewa kasar ta karya lagon cutar a halin yanzu. Wannan ya sa tuni harkokin kasuwanci da sauran hada-hadar yau da kullum sun fardado a cikin gidan kasar. Wani muhimmin bangare da ya ja hankalina shi ne fannin ayyukan hidimar aika sakonni kama daga sakonnin kar ta kwana zuwa abinci da sauran kayayyakin bukatu na yau da kullum. Ko da yake, amfani da sabbin dabarun fasahohin zamani wajen gudanar da harkokin kasuwanci sun taimaka matuka tun bayan da kasar ta rungumi tsarin cinikayya da ayyukan hidima na zamani ta hanyar amfani da kafafen intanet al'amurran tattalin arzikin kasar yake kara samun tagomashi. Alal misali fannin aika sakonni ya taka rawar a zo a gani matuka wajen habaka kudaden shiga ga kasar a daidai lokacin da duniya ke cigaba da fama da matsalar tabarbarewar tattalin arziki tun bayan bullar annobar COVID-19. Wasu alkaluma da hukumomin kasar Sin suka fitar sun nuna cewa, an samu matukar karuwar kudaden shiga da kuma bunkasuwar hada hadar ciniki na kamfanonin aika sakonni na kasar Sin a cikin watanni hudun farko na wannan shekara, duk da mummunan tasirin da annobar COVID-19 take cigaba da haifarwa ga sha'anin tattalin arzikin duniya.

A bisa alkaluman da hukumar aika sakonni ta kasar Sin ta ce, daga watan Janairu zuwa Afrilun wannan shekara, kudaden shigar fannin sun kai yuan biliyan 309.02, kwatankwacin dala biliyan 43.56, inda aka samu karin kashi 5.4 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara.

Bangaren aikewa da sakonnin kar ta kwana, wanda shi ne kashin bayan fannin hidimar aika sakonni, shi ma ya bada rahoton samun bunkasuwa a cikin watanni hudu, yayin da yawan kayayyakin da kamfanonin aika sakonni suka aika ya kai biliyan 19.03, wato ya karu sama da kashi 11.5% idan an kwatanta da makamancin lokacin bara. Jimillar kudaden shigar da wadannan kamfanoni suka samu ya karu da kashi 5.6% idan an kwatanta da makamancin lokacin bara wanda ya karu zuwa yuan biliyan 225.49. Hakika wannan ba karamar nasara bace da kasar ta cimma a daidai lokacin da duniya ke fuskantar tasirin illar annobar COVID-19 wacce ke cigaba da ta'azzara tattalin arzikin duniya baki.

Abin lura a nan shine wannan fannin na aika sakonni ya haifar da gagarumin cigaban tattalin arzikin kasar Sin gami da bunkasuwar kudaden shigar alummar kasa da kuma kyautata yanayin zaman rayuwar alummar Sinawa musamman a wannan lokacin da duniya ke fuskantar komadar tattalin arziki sakamakon bayyanar cutar numfashi ta COVID-19. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China