Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya yi kira ga kasa da kasa su taimakawa Afrika yaki da COVID-19
2020-05-16 16:29:20        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci al'ummomin kasa da kasa su inganta taimakonsu ga yakin da Afrika ke yi da COVID-19, tare da aiwatar da shirin kungiyar G20, na dakatar da harkokin biyan bashi ga kasashe mafiya fama da talauci.

Xi Jinping, ya bayyana haka ne a jiya, yayin da yake tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa.

Da yake bayyana yadda yaduwar COVID-19 ke kara kamari a Afrika, shugaba Xi ya ce karkashin shugabancin Cyril Ramaphosa, gwamnatin Afrika ta Kudu ta dauki jerin matakan tunkarar annobar da suka samar da kyawawan sakamako.

Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da goyon baya da taimakawa Afrika ta kudu iya karfinta, tare da karfafa hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakaninsu.

Ya ce a halin da ake ciki, Sin da nahiyar Afrika na bukatar goyon bayan juna fiye da kowanne lokaci domin yaki da cutar cikin hadin gwiwa da hada hannu wajen ganin bayan annobar, yana mai cewa, al'ummar Sinawa za su ci gaba da goyon bayan 'yan uwansu na Afrika.

A nasa bangaren, shugaba Ramaphosa ya ce, Afrika ta kudu da Sin na da buri iri guda a kan batutuwan da dama da kuma dangantaka mai karfi, inda ya ce, kasarsa na goyon bayan matsayar kasar Sin kan batun Taiwan da sauran batutuwan da suka shafi muhimman muradunta, kuma a shirye yake su yi aiki tare wajen kare muradun kasashen biyu.

Cyril Ramaphosa ya kuma yabawa kasar Sin bisa ci gaba da take yi wajen taimakawa kasashen Afrika, yana mai cewa, Sin ta kasance aminiyar Afrika ta kudu da sauran kasashen Afrika, kuma abokiyar hulda da za a iya dogaro da ita, a lokacin da ake fuskantar matsaloli da kalubale. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China