Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: COVID-19 za ta iya hallaka mutane kusan 190,000 a Afirka idan matakan yaki da cutar ba su yi nasara ba
2020-05-08 10:17:11        cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sanar a jiya Alhamis cewa, idan har matakan dakile cutar COVID-19 da aka dauka a nahiyar Afirka ba su yi aiki yadda ta kamata ba, akwai yiwuwar cutar ka iya halaka mutane tsakanin 83,000 zuwa 190,000, baya ga karin mutane miliyan 28 zuwa 44 da cutar ka iya harba.

Wani sabon bincike da ofishin shiyyar Afirka na hukumar ya gudanar, ya yi karin haske kan yiwuwar mutanen da cutar za ta shafa a nahiyar a shekarar farko na yaduwar annobar, bisa hasashe da aka yi kan alkaluman da suka shafi yanayin kasashe, da dalilai a bangaren zamantakewar jama'a da muhalli da ma illar da cutar ta haifar a halin yanzu.

Darektar hukumar mai kula da shiyyar Afirka, MatshidisoMoeti, ta bayyana cewa, yayin da ake hasashen cutar ba za ta yi kamari a nahiyar Afirka kamar yadda ta yi wasu sassan kasashen duniya ba, akwai yiwuwar cutar za ta yi muni a wuraren da ta bulla.

Jami'ar ta ce, COVID-19 za ta zama wani bangare na rayuwarmu nan da wasu shekaru masu yawa, har sai gwamnatoci da dama a shiyyar sun dauki managartan matakai. Don haka, akwai bukatar kasashen nahiyar su yi gwaji, da gano wadanda suka yi mu'amala, da killacewa da ma jinyar wadanda suka kamu da cutar. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China