Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta tura karin sojojin sama domin yaki da Boko Haram
2020-05-15 09:35:59        cri
Gwamnatin Najeriya za ta tura karin dakarun sojojin sama zuwa jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar domin taimakawa yakin da ake yi da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram, babban hafsan sojojin saman Najeriya Saddique Abubakar, shi ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis.

Yayin taron manema labarai, Abubakar ya ce za'a tura sojojin ne zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno, yankin da hare-haren Boko Haram ya fi kamari, ya ce matakin zai taimakawa dakarun sojojin saman kasar dake yaki da 'yan ta'addan.

Ya fadawa manema labarai cewa rundunar sojojin saman Najeriya tana ci gaba da gudanar da muhimmin aikin samar da dukkan abubuwan da ake bukata a ayyukan murkushe 'yan ta'addan.

Sama da wata guda ke nan, dakarun sojojin Najeriya ke ci gaba da kai munanan hare-hare a shiyyar arewa maso gabashin kasar da nufin kawo karshen ayyukan ta'addanci na mayakan Boko Haram da kungiyar masu neman kafa daular musulunci ta yammacin Afrika.

Abayomi Olonisakin, babban jami'in tsaron Najeriya ya bayar da umarni ga dakarun sojojin kasar da su hanzarta murkushe mayakan 'yan ta'adda bisa ga umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar tun da farko. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China