Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun ceto mutum 72 daga Boko Haram
2020-05-14 12:59:21        cri
A kalla mutane 72 ne suka samu 'yanci daga mayakan kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram, bayan da dakarun rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar da wasu hare hare kan mayakan kungiyar a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Wata majiya ta jami'an sojin Najeriyar ce ta tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Majiyar ta kuma ce galibin mutanen da sojojin suka kubutar mata ne da kananan yara.

Sojojin dai sun kaddamar da jerin hare hare ne kan sansanonin mayakan na Boko Haram, tun daga ranar 4 ga watan nan na Mayu. Majiyar ta kara da cewa, yayin wannan samame, an hallaka a kalla mayakan kungiyar 18, yayin da kuma wasu da dama suka tsere da harbin bindiga.

Bugu da kari, sojojin sun kwato tarin makamai da harsasai, da kayayyakin fada, da sauran na'urori da 'yan ta'addan na Boko Haram ke amfani da su. An kuma kama wasu masu agazawa kungiyar. (SAMINU)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China