Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba zai yiyu 'yan siyasar Amurka su cimma yunkurin kwace allurar rigakafin COVID-19 ba
2020-05-16 20:09:25        cri
Gabannin babban taron hukumar lafiya ta duniya karo na 73, manyan 'yan siyasa da kwararrun da abin ya shafa da yawansu ya kai sama da 140, wadanda ke kumshe da shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, da firayin ministan Pakistan Imran Khan, da tsohon firayin ministan Birtaniya Gordon Brown sun gabatar da wata budaddiyar wasika, inda suka yi kira da cewa, ya kamata a samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 ga daukacin a'ummun kasa da kasa ba tare da karbar kudi ba bayan an yi nasarar hada allurar, kana bai kamata a bar kasashen dake fama da talauci a baya ba.

An fitar da wannan budaddiyar wasikar ne saboda jagoran kamfanin hada magunguna na Faransa Sanofi ya bayyana kwanan baya cewa, Amurka za ta yi amfani da allurar riga kafin da za a samar kafin sauran kasashe, saboda ta samar da kudade mafi yawa kan aikin nazari na kamfanin. Tsokacinsa ya tayar da hankalin al'ummun kasa da kasa, daga baya kamfanin ya sake bayyanawa bisa matsin lambar gwamnatin Faransa da al'umma cewa, Amurka za ta iya amfani da allurar da za a samar a cikin kasar ta Amurka kafin sauran kasashe, amma ba za a samar da alluran da za a samar a kasar Faransa da sauran kasashen Turai ga Amurka kafin sauran kasashe ba.

Amurka, kasa mafi girma a duniya ta sake nuna yunkurinta na kwace allurar riga kafin cutar COVID-19 da ake nazarta a fadin duniya, lamarin da ya tayar da hankalin al'ummun kasa da kasa matuka.

An lura cewa, kwanan baya shugabannin Amurka sun sanar da cewa, "Za a kawar da kwayar cutar COVID-19, ba tare da bukatar samar da allurar riga kafi ba." Tsokacin ya nuna cewa, Amurka ba ta kula da nazarin allurar riga kafin, amma hakika gwamnatin Amurka tana kokari matuka domin kwace allurar kafin sauran kasashe.

A akasin haka, yayin wani taron samar da tallafin kudi na kasa da kasa da kungiyar tarayyar Turai ta shirya domin dakile annobar, bangarori daban daban sun samar da tallafin kudin da yawansa ya kai kudin Euro biliyan 7.4, domin gudanar da aikin nazari da hadawa da kuma raba allurar bisa adalci, amma gwamnatin Amurka wadda take dauka cewa, ita mai jagorancin kasashen duniya ce ba ta samar da ko kwabo ba.

Hakika gwamnatin Amurka tana cikin rudin kai saboda gaza dakile annobar, a don haka wasu 'yan siyasar kasar suna mai da hankali kan nazarin allurar riga kafin cutar, har suna son mallakar allurar su kadai, dalilin kuwa shi ne, wadannan 'yan siyasa suna son kubutar da kansu daga mawuyancin yanayin da suke ciki sakamakon gaza wajen daukar matakan da suka dace yayin dakile annobar, kafin babban zaben dake tafe, kana har kullum wadannan 'yan siyasa sun fi son samun karin kudi. Amma ba zai yiyu su cimma yunkurinsu ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China