Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bazuwar COVID-19 a fadin duniya laifin 'yan siyasar Amurka ne
2020-05-13 19:30:06        cri
Kwanan baya shahararren masanin Amurka Noam Chomsky ya bayyana yayin zantawarsa da manema labarai cewa, "Ya kamata shugabannin kasar Amurka su kula da hasarar rayukan al'ummun kasarsu, da ma na sauran al'ummun kasashen duniya." Kana ya yi nuni da cewa, shugabannin Amurka suna ta dora laifi kan wasu ne domin boye laifin da suka aikata kan al'ummun kasarsu.

Kamar yadda Noam Chomsky ya fada, a farkon barkewar annobar, duk da cewa masanan kandagarkin cututtuka na Amurka da hukumar lafiya ta duniya da kasar Sin da sauran sassan da abin ya shafa sun sha yin gargadi kan yaduwar annobar COVID-19, amma shugabannin Amurka ba su dauki matakan da suka dace ba, a sanadin haka, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar da mutanen da suka mutu a sakamakon cutar sun karu cikin sauri, abun takaici shi ne, a bisa irin wannan yanayi, 'yan siyasar Amurka ba su yi kokarin kandagarkin annobar ba, sai ma suka yi kokarin baza jita-jita domin dorawa wasu laifi.

Yanzu adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da annobar ya kai sama da miliyan 4, a cikin wadannan majinyata, daya bisa uku suna cikin Amurka, kan batun, mujallar The Atlantic ta wallafa wani rahoto, inda aka bayyana cewa, "Mu Amurkawa muna rayuwa a cikin wata kasa da ta gaza dakile annobar". A sa'i daya kuma, an lura cewa, yanzu Amurka ce kan gaba wajen yada cutar a ketare.

Kwanan baya jaridar National Post ta Canada ta gabatar da wani bayani cewa, masu yawon shakatawa 'yan asalin kasar Amurka ne sun shiga kasar ta Canada ne da kwayar cutar COVID-19. Cibiyar nazarin cutattuka ta kasar Japan ita ma ta bayyana cewa, sakamakon binciken da aka yi, ya nuna cewa, akwai yiwuwar kwayar cutar COVID-19 ta shiga Japan ne daga kasashen Turai. A halin da ake ciki yanzu, adadin mutanen da suka kamu da cutar a yankin Latin Amurka yana karuwa, sakamakon karuwar mutane masu dauke da kwayar cutar da suka shiga kasashen dake yankin daga Amurka. Gidan rediyon Columbia ya ba da rahoton cewa, a kasar Guatemala, wadanda suka kamu da cutar kaso 20 bisa dari makaurata ne da Amurka ta sallame su, duk wadannan shaidu sun tabbatar da cewa, wasu 'yan siyasar Amurka suna kawo cikas ga hadin gwiwar kasa da kasa a bangaren dakile annobar COVID-19, haka kuma suna lahanta tsaron kiwon lafiyar jama'a a fadin duniya.

A fim din Spider-Man na Amurka, an nuna cewa, "Mafi karfi shi ya kamata ya dauki nauyi mafi girma." Amma yanzu Amurka, a matsayinta na kasa mafi karfi a duniya ba ta sauke nauyin dake wuyanta ba, har ma tana kokarin lalata hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar dakile annobar, hakika akwai damuwa matuka kan yanayin da Amurka ke ciki, ba a san adadin al'ummun kasar da ke cikin kunci ba wadanda za su rasa rayukansu sakamakon cutar, amma an tabbatar da cewa, bazuwar COVID-19 a fadin duniya laifin 'yan siyasar Amurka ne.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China