Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta shiga mawuyancin yanayi yayin dakile COVID-19 sakamakon fifita siyasa fiye da kimiyya
2020-05-14 19:45:12        cri
Kwanan baya shehun malami a kwalejin nazarin harkokin gabashin Asiya ta jami'ar kasar Singapore Zheng Yongnian ya wallafa wani rahoto, inda ya bayyana cewa, yanzu haka annobar COVID-19 tana bazuwa a kasashe daban daban na fadin duniya, amma wasu kasashe ba su yi nasarar kawar da cutar ba, bambance siyasa da kimiyya, batu ne mai muhimmanci, saboda idan an bambance wadannan batutuwa biyu yadda ya kamata, to, ba ma kawai za a hana yaduwar annobar cikin lumana ba, har ma za a farfado da tattalin arzikin duniya lami lafiya. Shehun malamin ya kara da cewa, mahukuntan gwamnatin Amurka suna fifita siyasa fiye da kimiyya, wannan shi ne muhimmin dalili da ya sa kasar ta gaza dakile annobar.

Hakika an ga abun da shehun malami Zheng ya fada a farkon barkewar annobar, amma 'yan siyasar Amurka ba su saurari gargadin da hukumomin leken asiri da masana kiwon lafiyar jama'a na kasar da hukumar lafiya ta duniya da kasar Sin da sauran sassan da abin ya shafa suka yi ba, sun bata lokaci mai muhimmanci na hana yaduwar annobar, inda sun gaza dakile annobar a kan lokaci.

Masu lura da al'amuran yau da kullum sun yi nuni da cewa, dalilin da ya sa 'yan siyasar Amurka suka dora laifi kan wasu kasashe shi ne domin suna damuwa kan yadda matakan dakile annobar za su lalata tattalin arzikin kasar, haka kuma za su yi tasiri ga babban zaben kasar dake tafe, a don haka sun yi biris da yaduwar annobar, tare kuma da dora laifi ga wasu.

A sa'i daya kuma, sun siyasantar da annobar, domin boye laifinsu na gaza dakile annobar, har sun yada jita-jitar cewa, kwayar cutar COVID-19 ta fito ne daga dakin gwajin kasar Sin, duk da cewa, kwararrun kimiyya sun riga sun cimma matsaya kan asalin kwayar cutar.

Amma 'yan siyasar Amurka ba su cimma burinsu ba, inda suka jefa kasarsu cikin mawuyancin yanayi.

Annoba tamkar madubi ne, dake nuna karfin gwamnatin kasa, kamar yadda ake ganin abin da ke faruwa a kasar ta Amurka, duk da cewa, Amurka kasa ce da take bayyana cewa tana ba da muhimmanci kan kimiyya, amma 'yan siyasar kasar sun rushe kimiyya da hankali, har wasu kafofin watsa labaran kasar sun yi daga murya cewa, "Muna rayuwa ne a cikin kasar da ta gaza dakile annobar." Ana iya cewa, Amurkawa suna fuskantar hadarin hasarar rayuwa sakamakon son kai na wasu 'yan siyasa, kamar yadda shehun malami Zheng Yongnian ya bayyana cewa, babu wata kasa kamar Amurka, inda manyan jami'ai da 'yan majalisar dokoki suke mai da hankali matuka kan dora laifi ga kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China