2020-05-15 20:09:56 cri |
Sakataren taron tsaro na tarayyar Rasha Nikolay Platonovich Patrushev shi ma ya fayyace cewa, kawo yanzu adadin dakunan gwajin halittun da Amurka ta gina a fadin duniya ya riga ya kai sama da 200, kana an lura cewa, annoba mai hadari ta taba yaduwa a wuraren da Amurka ta gina dakunan gwajin halittun nata, duk wadannan sun sanya tsoro matuka kan tsaron wadannan dakunan gwaje-gwaje.
Dakin gwajin halittu na Detrick dake jihar Maryland ta Amurka, shi ne sansani mafi girma dake kasar inda ake samar da makamai masu guba, ana daukar sansanin a matsayin "cibiyar gwaji mafi duhu" na gwamnatin Amurka, ko "sansanin gwajin sinadarai masu guba da kawar da hankalin mutane na hukumar leken asiri ta Amurka". A watan Yulin bara, ba zato ba tsammani, cibiyar CDC ta Amurka ta rufe dakin gwajin bisa dalilin tsaron kasa, kuma ta ki sanar da bayanan da abin ya shafa.
Kana jaridar New York Times ta fayyace cewa, abubuwan da ake nazari a cikin dakin gwajin sun hada da wasu halittu masu hadari wadanda za su lahanta lafiyar mutane da dabbobi da tsirrai ko kayayyakin da ake samarwa da dabbobi da tsirrai, abun da ya fi tsorata jama'a shi ne, bayan da aka rufe dakin binciken, an tarar da cewa, cutar tabar lantarki ta barke a wata unguwa dake kusa da dakin gwajin, alamun cutar sun yi kama da alamun cutar COVID-19, amma yanzu 'yan siyasar Amurka wadanda suke ta baza jita-jita sun yi shiru kan batun.
Rahotannin sun nuna cewa, Amurka ta gina wasu dakunan gwajin halittu a kasashe da dama a cikin tsohuwar tarayyar Soviet Union, wasu kuma suna kasashen dake kudu maso gabashin Asiya, da kuma nahiyar Afirka. Abun mamaki shi ne Amurka ta yi shiru kan yadda take amfani da aikin da suke yi da ma tsaro na wadannan dakunan gwajin.
Yanzu haka matakan da 'yan siyasar Amurka suka dauka sun nuna cewa, kila ne Amurka tana kirkirar kwayar cutar da za ta haifar da cututtuka masu hadari a dakunan gwaje-gwaje dake ketare.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China