Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan siyasar Amurka suna canja masifar da ta bullo daga indallahi zuwa masifar da suka haifar
2020-05-12 19:34:51        cri
Kwanan baya tsohon jakadan kasar Amurka dake kasar Sin Max Baucus ya bayyana cewa, yanzu a Amurka, daukacin mutane wadanda suke nuna ra'ayin goyon bayan kasar Sin suna damuwa matuka saboda kila su rasa rayukan su, kana ya yi nuni da cewa, gwamnatin Amurka tana bayyana ra'ayin kyamar kasar Sin, duk da cewa, Amurkawa da dama sun san bai kamata ba a soki kasar Sin bisa dalilai marasa tushe, amma suna jin tsoro, a don haka sun yi shiru, ba sa bayyana ra'ayinsu

Wasu 'yan siyasar Amurka masu ra'ayin cacar baka, suna shafawa kasar Sin bakin fenti, ta hanyar dora mata laifin gaza daukar matakan da suka dace yayin dakile annobar COVID-19, wadannan 'yan siyasa sun yi biris da rayukan al'ummun kasar, suna mayar da hankali wajen kare muradun kansu, duk wadannan za su jefa kasar ta Amurka cikin mawuyaci hali.

Hakika tun farkon barkewar annobar, gwamnatin Amurka ta nuna halinta na son kai, ta yi biris da gargadi da bayanan da kasar Sin ta fitar, ta kuma taba gaya wa al'ummun kasar cewa, annobar COVID-19 babbar cutar mura ce kawai, babu bukata a sa marufin baki da hanci, har ta yi farin ciki saboda tana ganin cewa, annobar da ta barke a kasar Sin, wata dama ce ga kamfanonin Amurka, da ma yadda guraben ayyukan yi za su dawo a kasar.

Masanan kasa da kasa da abin ya shafa sun nuna cewa, matakan da gwamnatin Amurka ta dauka a halin yanzu suna canja wannan masifar da ta bulla daga indallahi zuwa masifar da 'yan siyasa suka haifar. Masani kan yaduwar cututtuka na jami'ar Imperial ta London Britta L. Jewell ya wallafa wani rahoto a jaridar New York Times, inda ya bayyana cewa, da gwamnatin Amurka ta fara daukar matakin killace jama'a daga ranar 2 ga watan Maris a maimakon ranar 16 ga watan, da adadin mace-mace a kasar sakamakon annobar zai ragu da kaso 90 bisa dari, haka kuma idan da an fara aiwatar da dokar zama a gida a kasar daga ranar 9 ga watan Maris, adadin zai ragu da kaso 60 bisa dari.

A bayyane an lura cewa, zai yi wahala wasu 'yan siyasar Amurka wadanda suka kamu da kwayar siyasa su warke daga cutar tabuwan hankali, amma huldar dake tsakanin Sin da Amurka wadda ta samu ci gaba a cikin shekaru sama da 40 da suka gabata ta shaida cewa, hadin kai zai amfanin sassan biyu, fito na fito za ta lalata su duka, hadin gwiwa ita ce hanya daya kacal da ta dace sassan biyu za su bi, ya dace Sin da Amurka su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu yayin da suke kokarin dakile annobar, har kullum kasar Sin tana nacewa kan matsayar hadin gwiwa, ana sa ran wadannan 'yan siyasa za su fahimci yanayin da kasarsu ke ciki, su daina salwantar da rayukan al'ummun kasar ta Amurka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China