Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana sa ran 'yan siyasar Amurka su daina yaudarar al'ummun kasar saboda hakan zai kara hasarar rayuka a kasar
2020-05-11 21:37:25        cri
Jiya Lahadi jaridar New York Times ta Amurka ta wallafa wani rahoto cewa, hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka FBI da ma'aikatar tsaron kasar suna shirya fitar da wani gargadi, inda za su sanar da cewa, "Masu satar bayanai ta yanar gizo na kasar Sin suna kokarin satar sakamakon nazarin da Amurka ta samu a bangarorin samar da maganin riga kafin annobar COVID-19 da jinyar masu kamuwa da cutar." Duk da cewa, 'yan siyasar Amurka suna ta baza jita-jitar da suka kitsa, amma har kullum ba su cimma manufarsu ba.

Hakika ya dace a kira Amurka kasa mai satar bayanai, kasar Sin tana shan fama da kalubalen da masu satar bayanan yanar gizo na Amurka suke haifar mata. Kwanan baya wani kamfanin tsaron yanar gizo na kasar Sin ya fayyace cewa, kungiyar masu satar bayanai ta APT-C-39 karkashin jagorancin hukumar liken asirin Amurka ta CIA tana kai hari kan tsarin intanet na kasar Sin har tsawon shekaru sama da goma. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, Amurka ta saba dokokin kasa da kasa da ka'idojin huldar kasa da kasa a fili, ta kai hari da sa ido da kuma satar bayanan tsarin intanet na gwamnatoci da kamfanoni da daidaikun mutane na sauran kasashen duniya, lamarin da ya kasance sirri a fili.

Amma ba zai yiyu ba a boye hakikanin abubuwa, kasar Sin wadda ita ce kasa ta farko da ta sanar da yanayin da take ciki wajen dakile annobar COVID-19, har kullum tana gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashe ba tare da rufa-rufa ba. Tun bayan barkewar annobar, nan da nan kasar Sin ta raba fasahohin da ta samu a bangaren, ana iya cewa, ta taka rawar gani wajen dakile annobar a fadin duniya.

A bayyane an lura cewa, kasar Sin ta kasance a sahun gaba ta fuskar nazarin maganin riga kafin annobar da matakan jinyar masu kamuwa da cutar, kamar yadda masu nazarin al'amuran yau da kullum suka bayyana, "A matsayinta na kasa mafi kwarewa wajen nazarin kwayar cutar COVID-19, kasar Sin ba ta bukatar satar bayanan Amurka."

Yanzu haka annobar tana ci gaba da bazuwa cikin sauri a fadin duniya, maganin riga kafin cutar shi ne makami mafi karfi da zai iya hana yaduwarta, a don haka kwararrun kimiyya dake sassan daban daban na duniya suna dukufa kan aikin nazarin da abin ya shafa ba rana ba dare, dalilin da ya sa haka shi ne domin rayukan bil Adama sun fi komai muhimmanci, ana fatan wasu 'yan siyasar Amurka za su daina baza jita-jitar marasa tushe, su kuma daina yaudarar al'ummun Amurka saboda hakan zai kara hasarar rayuka a kasar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China