Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sahalewa Bankin kasar Sin bayar da adadin da ya kai yuan miliyan 200 na hannun jari mafi daraja a kasashen waje
2019-07-06 16:44:28        cri
An sahalewa Bankin kasar Sin BOC, kai wa yuan biliyan 20 (kwatankwacin dala biliyan 2.9) ko kuma kwatankwacin adadin a takardar kudaden ketare, ta hanyar sayar da hannun jari mafi daraja a kasashen waje

Wata sanarwa da bankin ya fitar, ta ce hukumar kula da bankuna da inshora ta kasar Sin ce ta sahale masa shirinsa na bayar da abun da bai fi yuan miliyan 200 ba, na hannun jari mafi daraja a kasuwannin kasashen waje.

Hannun jari mafi daraja da na gama gari, su ne nau'ikan hannayen jari 2 da kamfanoni ke ba masu zuba jari. Masu hannayen jari mafi daraja na da wasu hakkoki na musamman fiye da masu hannayen jari na gama gari, wajen rarraba riba da kadadori.

Ba kamar jarin gama gari ba, hannun jari mafi daraja na aiki ne kamar takardar lamuni. Kamfanonin tantance kimar basussuka ne ke tabbatar da matsayinsu, kuma sauyin kudin ruwa na tasiri akan farashinsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China