Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kungiyar WTO zai yi murabus a bana
2020-05-15 10:43:57        cri

Darakta Janar na Kungiyar cinikayya ta duniya WTO, Roberto Azevedo, ya ce zai yi murabus daga mukaminsa a karshen watan Augustan bana, kafin wa'adin aikinsa ya kare.

Cikin wata sanarwa da aka wallafa a jiya, Roberto Azevedo ya ce a watan Augustan bana, zai kammala cika shekaru 7 a matsayin Darakta Janar na WTO. Kuma ya yanke shawarar zai yi murabus a ranar 31 ga watan Augustan, shekara guda kafin kammala wa'adinsa na biyu a mukamin.

Ya ce wannan ba mataki ne da ya dauka da wasa ba. Yana mai cewa, tsakanin aiwatar da dokar kulle da tiyatar da aka yi masa a gwiwa, ya samu lokaci sosai na yin tunani. Kuma ya kai ga wannan matsaya ne bayan tattaunawa mai tsawo da iyalinsa. Ya kuma musanta matakin nasa na da alaka da batutuwan lafiya da siyasa.

Ya ce mataki ne na kashin kansa da kuma iyalinsa, yana mai cewa ya yi ammana matakin shi ne mafi dacewa ga kungiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China