Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kai Amurka kara gaban WTO kan batun kara harajin kwastom
2019-09-03 12:46:14        cri
Gwamnatin kasar Sin ta sanar a jiya Litinin cewa, ta shigar da kara a gaban kungiyar ciniki ta duniya WTO inda take kalubalantar Amurka game da matakin data dauka na aiwatar da karin harajin kwastam na kashi 15% kan kayayyakin da kudinsu ya kai dala biliyan 300 da ake shigo dasu daga kasar Sin wanda ya fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumba.

Wata sanarwar da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar ta bayyana cewa, harajin kwastam din da Amurkar ta kara ya sabawa daidaito da shugabannin kasashen biyu suka cimma a birnin Osaka, sanarwar tace, kasar Sin ta nuna kin amincewarta da babbar murya kuma tana Allah wadai da karin harajin kwastam din da Amurkar ta aiwatar.

Sanarwar ta kara da cewa, kasar Sin zata tabbatar da kiyaye hakkokinta da moriyarta kuma ta nanata aniyarta na cigaba da aiwatar da tsarin ciniki na gamayyar kasa da kasa kana da mutunta dokokin kasuwanci na kasa da kasa wadanda suka dace da yanayin dokokin kungiyar ciniki ta duniya WTO.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China