Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta fito da shawararta kan yadda za a daidaita matsalar WTO
2019-12-12 19:22:37        cri

Yau a nan birnin Beijing mai magana da yawun ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya yi tsokaci game da yadda kotun sauraron kara ta kungiyar cinikayyar duniya ta daina zaman sauraron kara, inda ya bayyana cewa, yanzu tsarin daidaita rikici na kungiyar cinikayyar duniya ya daina aiki, kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta kan wannan batu.

Gao Feng ya jaddada cewa, kasar Sin tana ganin cewa, tsarin daidaita rikici ta hanyar amfani da kungiyar cinikayyar duniya yana da muhimmanci matuka wajen kiyaye tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da tsarin cinikayyar duniya wanda aka tsara bisa tushen adalci, yanzu gaba daya adadin kararrakin da aka gabatar wa kotun ya kai 15, kuma hudu daga cikinsu an riga an fara sauraron su, saura 11 ba a gabatar da su ba tukuna.

Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da aka tsara bisa adalci, haka kuma za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da kasashe daban daban suke yi domin maido da aikin kotun sauraron kara ta kungiyar. A sa'i daya kuma, kasar Sin tana yin nazari domin fito da shawararta a lokacin da ya dace domin daidaita matsalar a kan lokaci.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China