Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta nuna rashin jin dadi kan yadda kotun sauraron kara ta WTO ta daina aiki
2019-12-11 19:23:26        cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta nuna rashin jin dadinta saboda yadda kotun sauraron kara ta kungiyar cinikayyar duniya wato WTO ta daina aiki, bisa dalilin ra'ayin bangaranci da ba da kariya na Amurka.

Rahotanni sun ce, Amurka ta hana a yi zabi da kuma nada sabon alkalin kotun, tun daga yau kotun za ta daina zaman sauraron kara, saboda karancin alkalai, bayan da alkalai biyu suka kammala wa'adin aikinsu jiya.

Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin ta lura cewa, mambobin kungiyar WTO da yawansu ya kai 117 sun yi kira a shirya zaben alkalai nan take, kasar Sin tana son hada kai tare da su domin daidaita matsalar da ake fuskanta.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China