Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dan siyasar Amurka ya musunta halin kishin kasa na Sin da gangan
2020-05-10 17:27:33        cri
Kwanan baya, mataimakin mai taimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa Matthew Pottinger wanda shi ne babban jami'in kasar da yake dauka cewa, ya fahimci kasar Sin sosai, ya gabatar da wani rahoto da Sinanci a cibiyar Miller ta jami'ar Virginia, inda ya bayyana cewa, halin kishin kasa wato halin zanga-zangar da aka yi a ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919 na kasar Sin shi ne tunanin ikon fararen hula wato ya dace fararen hula su rike mulkin kasa, kana ya yi suka kan hanyar raya kasa ta kasar Sin, duk da cewa ya yi jawabi da Sinanci, amma daga abubuwan da ya bayyana a cikin jawabinsa, an lura cewa, bai san kome ba kan tarihi da yanayin da jama'ar kasar Sin, har an gano mugun nufinsa, hakika makasudin yin zanga-zangar ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919 shi ne, domin yin kira ga al'ummun kasar da su sanya kokari domin ceton kasarsu daga zalunci.

A tarihin kasar Sin, halin kishin kasa da ci gaba da demokuradiya da kimiyya na zanga-zangar ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919 ya sa kaimi kan matasan kasar Sin daga zuriya zuwa zuriya domin su taka rawa kan ci gaban kasa, a bayyane an lura cewa, ma'anar halin mafi muhimmanci ita ce, kishin kasa, ba ikon fararen hula ba.

Yanzu haka ana fama da annobar COVID-19, daukacin jama'ar kasar Sin suna hada kai suna sanya kokari tare, har sun samu babbar nasara wajen dakile annobar, hakika a daidai wannan lokaci mai hadari, kowa da kowa a kasar, musamman ma matasan kasar sun ba da gudummowa gwargwadon karfinsu, duk wadannan sun nunawa al'ummomin kasa da kasa halin kishin kasa na zanga-zangar ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919.

Rahotannin sun nuna cewa, a cikin masu aikin jinya wadanda suka je lardin Hubei domin ba da tallafi da yawansu ya kai sama da dubu 42, sama da dubu 12 matasa ne wadanda aka haife su bayan shekarar 1990, wasu kuwa aka haife su bayan shekarar 1995 ko 2000, ana iya cewa, matasan kasar Sin matasa ne masu halin kishin kasa.

Ana son tambayar Mista Matthew Pottinger, ta yaya kake yaudare jama'a, ta hanyar baza jita-jita, ko ka san ina dalilin da ya sa Amurka wadda kasa ce mafi karfi wajen kimiyya da fasaha ta gaza daukan matakan da suka dace yayin da take kokarin hana yaduwar annobar COVID-19? Ko ka san lokacin da mutum na farko a Amurka ya kamu da cutar? Ko ka san yadda gwamnatin Amurka ta bata lokacin dakile annobar har tsawon watanni biyu? To, ina kimiyya da demokuradiya suke? Wane ne ke yaudare jama'ar Amurka?

Yunkurin boye asalin kimiyya shi ne domin samun moriyar kansu, yayin babban zaben dake tafe. Amma babu wanda zai boye hakikanin abun da ya faru a kasar, wato Amurkawa da dama sun rasa rayukansu a sakamakon gaza daukan matakan da suka dace wajen hana yaduwar annobar, ya dace 'yan siyasar Amurka su daina yin "gasar ikon mulkin kasa", su daina yaudare al'ummomin kasa da kasa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China