Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin bata amince da duk wata kasa dake da huldar jakadanci da ita ta yi duk wata mu'amala ta bangaren gwamnati da yankin Taiwan ba
2020-01-12 20:28:37        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya amsa tambayar da aka yi masa yau Lahadi, game da sakon taya murna da manyan jami'an gwamnati na wasu kasashe suka aika ga wadda ta ci zaben yankin Taiwan, inda ya ce, zaben da aka gudanar batun da ya shafi wani yanki na kasar Sin ne. Abun da wasu kasashen suka yi ya sabawa manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, kuma kasar Sin na matukar adawa gami da kin yarda da wannan, har ta riga ta gabatar da korafinta ga kasashen da abun ya shafa.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China