Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin kai ne hanya daya tilo mafi dacewa wajen warware matsala
2020-05-10 16:14:43        cri

A ranar 8 ga wata, bisa gayyatar da aka yi masa, mataimakin firaministan kasar Sin, kuma mai jagorancin tattaunawar tattalin arziki a tsakanin kasashen Sin da Amurka na bangaren Sin, Liu He ya zanta da wakilin cinikayya na Amurka Robert Lighthizer, da ministan kudin kasar Robert Mnuchin ta wayar tarho, inda bangarorin biyu suka bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su karfafa hadin kai a fannonin tattalin aiziki da kiwon lafiyar al'umma, kana da kokarin samar da muhalli mai kyau don tabbatar da yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya bisa matakin farko a tsakanin kasashen biyu, baya ga haka bangarorin biyu su amince da kiyaye cudanya a fannin.

Wannan ne karo na farko da masu jagorantar tattaunawa na kasashen biyu suka buga wayar tarho bayan kusan rabin shekara da aka cimma yarjejeniyar. A yayin da ake ciki na tinkarar yaduwar annobar COVID-19 a duniya baki daya, irin zantawar na da ma'ana kwarai.

A cikin zantawar da masu jagorantar tattaunawar kasashen biyu suka yi har fiye da sau goma a cikin shekaru biyu da suka gabata, wannan ne karo na farko da suka gabatar da "Karfafa hadin kai a fannonin tattalin arziki da kiwon lafiyar al'umma. Hakan ake iya gano cewa, lallai yaduwar annobar ta kawo babbar illa ga tattalin arzikin daukacin duniya, tare kuma da kawo rashin tabbas ga tabbatar da yarjejeniyar tattalin arziki da bangarorin biyu suka cimma.

Baya ga haka, bayanin da aka yi a yayin zantawar na "yi kokarin samar da muhalli mai kyau na cimma yarjejeniyar bisa mataki na farko" shi ma yana da ma'anarsa. A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, wasu 'yan siyasar kasar Amurka sun yi fatali da sadaukarwar da Sin ta yi kan aikin yakar annobar a duniya baki daya, sun kuma yi zargi kan kasar Sin ba tare da yin la'akari da hakikanin halin aikin yakar cutar.

Kamar yadda aka sani, cutar COVID-19 babbar barazana ce ga duniya, kuma kalubalen bai daya da duk dan Adam ke fuskanta. A matsayinta na kasa ta farko da ta sanar da annobar ga kasashen duniya, kuma kasa ta farko wajen yakar cutar, kasar Sin ta tayar da jama'arta tsaye, bayan namijin kokarin da ta yi, ta cimma nasarar dakile cutar a kasar, kana ta samar da fasahohi masu inganci ga aikin yakar cutar a duniya.

Masu idon basira suna sane cewa, wasu 'yan siyasar Amurka sun dauki wadancan matakan ne sakamakon matsayin da suke tsayawa na mayar da zaben kasar a gaban rayuwar al'ummarta.

Cuta ba ta san kasa ba, annoba ba ta san kabila ba, ko a fannin tattalin arziki ko kuma a fannin tinkarar annoba, karfafa hadin kai a tsakanin kasashen Sin da Amurka ne hanya daya kacal da ya kamata a bi. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China