Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya aika sakon gaisuwa ga ma'aikatan nas-nas gabanin ranar nas-nas ta duniya
2020-05-11 19:21:50        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban rundunar askarawar kasar, ya aika sakon gaisuwa ga daukacin ma'aikatan nas-nas dake sassan kasar, gabanin ranar ma'aikatan nas-nas ta duniya da za a yi bikinta gobe Talata 12 ga watan Mayu.

Xi ya ce, tun lokacin da annobar COVID-19 ta barke, ba tare da wata ba, ma'aikatan nas-nas da dama sun shiga aikin yaki da wannan annoba, kuma sun nuna cewa, za a iya dogara a kansu. Haka kuma sun sadaukar da kansu wajen ganin bayan wannan annoba a ciki da wajen kasar nan, abin da ke nuna ruhin mutuntawa da kare rayuka, jinyar wadanda suka kamu da cutar da ceton rayuka tare da sadaukar da kai kan wannan aiki.

Shugaba Xi ya kuma bayyana fatan cewa, ma'aikatan nas-nas, za su isar da wannan al'ada mai kyau da yayata akidar jin kai da kara ba da gudummawa ga ci gaban harkokin kiwon lafiyar kasar Sin da lafiyar al'ummar duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China