Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu dauke da COVID-19 a Najeriya ya haura 3,000
2020-05-07 20:20:26        cri
Cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya NCDC, ta ce an samu karuwar mutane 195 da suka harbu da cutar numfashi ta COVID-19 zuwa daren jiya Laraba, wanda hakan ya daga jimillar wadanda cutar ta harba a kasar zuwa mutum 3,145, ciki hadda mutane 103 da ta hallaka, da kuma 534 da suka warke bayan kamuwa da ita.

Cikin wata sanarwa da NCDC ta fitar, ta ce an samu sabbin masu kamuwa da cutar ne a jihohin kasar 13, ciki hadda birnin Abuja fadar mulkin kasar. Sanarwar ta kara da cewa, karuwar cibiyoyin gwaji a sassan kasar, ya sa ana kara gano masu kamuwa da wannan cuta.

Mahukuntan Najeriyar dai na ta fadi tashin ganin sun dakile yaduwar wannan annoba, tun bayan bullar ta a karon farko, a ranar 27 ga watan Fabarairu, a kasar dake kan gaba wajen yawan al'umma a daukacin nahiyar Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China