Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu COVID-19 a Najeriya ya karu zuwa 2,950
2020-05-06 20:19:05        cri
Hukumar dake yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, ta ce an samu karin mutane 148 da suka harbu da cutar numfashi ta COVID-19, wanda hakan ya sanya jimillar masu dauke da cutar karuwa zuwa mutum 2,950. Kaza lika adadin wadanda cutar ta hallaka, shi ma ya karu zuwa mutum 98, bayan da aka samu karin mutum 6 da cutar ta hallaka ya zuwa daren jiya Talata.

A daya bangaren kuma, adadin wadanda suka warke bayan shan fama da cutar, shi ma ya karu zuwa mutum 481, yayin da kuma masu fama da ita a yanzu haka suka kai mutum 2,371.

NCDC ta ce karin cibiyoyin gwajin wannan cuta da ake kafawa a sassan kasar ne, ya ba da damar gano karin masu dauke da cutar. Har ila yau hukumar tana kara matsa kaimin yaki da wannan cuta, ta hanyar hada karfi da karin abokan huldarta, wadanda ke taimakawa wajen tsaya dabarun dakile ta, a matakai na jihohi da na tarayya.

Bugu da kari, NCDC na ci gaba da tura jami'an lafiya, da kayan aiki ga jihohin da wannan cuta ke addaba. Tana kuma tsara samar da karin dukkanin hidimomi da ake bukata, da tanaji domin kaucewa fadadar annobar a dukkanin fannoni. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China