Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya zama tilas a bar kimiyya ta yi aikinta yayin da ake yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19
2020-05-02 19:46:49        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, yadda ake siyasantar da batun asalin kwayar cutar COVID-19, ya saba asalin tsarin binciken kimiyya, kana bai dace da kokarin da duniya ke yi na yaki da annobar ba.

Geng ya bayyana haka ne a kwanan baya yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa a taron manema labarai da aka saba shiryawa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, kan ko kasar Sin tana duba yiwuwar gudanar da bincike na kashin kanta game da asalin kwayar cutar, inda ya jaddada cewa, batun gano asalin kwayar cuta, batu ne na kimiyya wanda ya kamata a damka shi ga masana kimiyya da kwararru domin su yi nazari, ba wai wasu su rika shaci fadi game da asalin kwayar cutar ba.

Ko hada kwayar cutar aka yi, ko a'a, tuni manyan cibiyoyin nazarin kimiyya na kasa da kasa suka riga suka ba da tabbatacciyar amsa. A ranar 18 ga watan Fabrairun bana ne, manyan masana kimiyya da yawansu ya kai 27, suka fitar da wata hadaddiyar sanarwa a shahararriyar mujallar The Lancent, inda suka yi watsi da ra'ayin kirkirar kwayar cutar COVID-19, har ma shahararen masanin nazarin cututtuka masu yaduwa na kasar Amurka Anthony S. Fauci ya bayyana cewa, dabbobi ne suka yada kwayar cutar ga bil Adama, yana mai cewa ba kirkirar ta aka yi a dakin gwaji ba.

Hakika dai ana bukatar tattara dimbin bayanan halittu da abubuwan shaida dangane da yaduwar annobar cutar, wadanda suke iya tabbatar da juna, ta yadda za a iya tabbatar da asalin wannan kwayar cuta a karshe. A sa'i daya kuma tabbatar da asalin kwayar cuta, wani batu ne mai wuyar warwarewa a fannin kimiyya. A kan dauki dogon lokaci ana gudanar da nazari, don tabbatar da asalin kwayar cutar. Ya zuwa yanzu, masu ilmin kimiyya na kasa da kasa ba su iya tabbatar da yadda annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta fara yaduwa a duniya ba. Don haka babu abubuwan shaida a fannin kimiyya da suka iya tabbatar da asalin kwayar cutar ta COVID-19, kana yanke hukunci kan asalinta bai dace da ruhun kimiyya ba.

Yanzu haka dai daukacin bil Adama suna fama da annobar, kuma hadin kai shi ne abu mafi muhimmanci, idan ana son ganin bayanta. Dole ne 'yan siyasar wasu kasashe wadanda suke siyasantar da annobar su kara fahimta cewa, ba za su cimma yunkurinsu na bata sunan kasar Sin ba, kuma dora laifi ga wasu, ba zai iya sassauta mawuyacin yanayi da wannan annoba mai tsanani ta jefa kasashensu ba. Kamata ya yi kasashen duniya su mai da hankali kan dakilewa da kandagarkin yaduwar annobar da ceton rayukan mutane. Sanya siyasa kan batun tabbatar da asalin kwayar cutar zai kawo cikas ga hadin gwiwar da ke tsakanin kasa da kasa, zai kuma haifar da rashin aminci tsakanin kasashen duniya. A daidai wannan lokaci, kamata ya yi mu bar kimiyya ta yi aikinta yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China