Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yaki da COVID -19: Kowa na da rawar takawa
2020-04-28 16:22:28        cri

Al'ummar duniya na ci gaba da yaki da cutar COVID-19, inda kowacce kasa ta zage damtse wajen daukar irin managartan matakan da take ganin sun dace da ita. Yayin da aka samu nasarar dakile yaduwar cutar da kula da wadanda suka kamu a kasar Sin, yanzu cutar take kara shiga nahiyar Afrika da sauran wasu kasashen sassan duniya, cikinsu har da wadanda suka gaza amfani da damar da Sin ta samar na tunkarar cutar tun bayan bullarta da gano hadarin dake tattare da ita.

Nahiyar Afrika ta kasance wurin da masana suka yi hasashen ka iya zama inda cutar ta fi kamari a nan gaba kadan, bisa la'akari da yawan al'umma da rashin ci gaba. Sai dai, duk da cewa cutar na ci gaba da bazuwa kamar wutar daji, gwamnatocin nahiyar sun dukufa iya karfinsu wajen ganin sun ga bayanta.

Nijeriya ma ba a bar ta a baya ba, inda gwamnatocin tarayya da na jihohi suka dauki ingantattun matakai daban-daban na ganin sun dakile yaduwar cutar a tsakanin al'ummominsu.

Ya zuwa jiya Litinin da daddare, hukumar hana yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta kasar NCDC, ta ce jimilar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 1337, bayan samun wasu karin mutane 64 da suka harbu a jiyan. Baya ga haka, akwai mutane 255 da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti, yayin da wasu 40 suka mutu sanadiyyar cutar.

A karo na 3 tun bayan samun bullar cutar na farko a ranar 27 ga watan Fabreru, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya gabatar da jawabi da aka watsa kai tsaye ga al'ummar kasar ta kafofin yada labarai, dangane da matakan da gwamnatinsa take dauka na yaki da cutar. Ya ce a makonni biyu da suka gabata, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya tsaya ne kan 323 a jihohi 20 na kasar da birnin tarayya Abuja. Amma ya zuwa safiyar jiya Litinin, adadin ya karu zuwa 1,273 tare da bulla a karin wasu jihohi 12.

Hasashen da aka yi a baya, ya nuna cewa cikin watanni biyu na farkon bullar cutar, kimanin mutane 2000 ne za su harbu bayan samun bullar cutar na farko. A cewar shugaban, wannan na nufin duk da karuwar adadin wadanda suka kamun, kwalliya tana biyan kudin sabulu dangane da matakan da gwamnatinsa take dauka.

Matakan kulle da na hana taron jama'a da wayar da kan jama'a kan matakan kariya da rufe iyakokin kasar da na jihohi da yin gwaji da tabbatar bibiyar wadanda suka kamu da wadanda suka yi cudanya da su, ya taimaka sosai wajen rage yaduwar cutar a kasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika, idan aka yi la'akari da hasashen da aka yi. Baya ga haka, tallafin kayayyaki da kwararru daga kungiyoyi da daidaikun jama'a da hukumomi da kasashe, kamar Sin suka ba kasar, su ma sun taka muhimmiyar rawa wajen kara karfin kasar na tunkarar wannan annoba.

A wannan gaba ne kuma, shugaban ya sanar da matakin fara sassauta dokar kulle a babban birnin kasar da jihohin Lagos da Ogun da aka fara kakabawa dokar tun farkon bullar cutar. Inda gwamnatin za ta fara aiwatar da sabbin matakai da suka hada da na takaita zirga-zirga daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe, da hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi da tilasta sanya marufin hanci da baki da nisantar juna tsakanin mutane da sauran wasu matakai na farfado da harkokin tattalin arziki.

Ba abu ne mai yuwuwa Gwamnati ita kadai ta iya yaki da wannan annoba mai sarkakiya ba. Kamar yadda mallam Bahuashe kan ce, hannu daya, ba ya daukar jinka; akwai bukatar kungiyoyi da daidaikun mutane da ma daukacin al'umma su hada hannu wajen ganin bayan wannan cuta. Na farko, kiyaye ka'idojin doka muhimmiyar hanya ce ta dakile yaduwar wannan cutar. Misalai, mun gani a kasar Sin yadda aka dakile wannan annoba, bisa goyon baya da al'umma suka bayar da martabawa da girmama tanade-tanaden doka da matakan gwamnati. Gwamnatin kasar Sin ba ta tsaya wata wata ba wajen sanar da dokar kulle a inda aka fi samun yawan masu cutar, su ma kuma al'ummarta ba su bata lokaci, ko yin biris da wannan doka ba. Wannan ya nuna cewa hadin kai tsakanin bangarori daban-daban ya taimaka gaya wajen samun nasarar hana yaduwar cutar a kasar. Wanda darasi ne da ya kamata kasashen duniya su dauka.

Idan a ce al'ummomi a Nijeriya za su kiyaye irin wadannan dokoki da ka'idoji da gwamnati ke shimfidawa, to babu makawa za a ga bayan wannan cuta. Sai an sha wuya ake jin dadi. Hakuri da juriya da sadaukarwa, su ne za su kai al'umma ga murmusawa a nan gaba.

Hakika matakan za su zama tamkar matsi ga harkokin zamantakewa da na tattalin arziki, amma amfanin da za su yi, ya shafe duk wata matsala da ake ganin za su haifar. Ina amfanin rayuwa babu lafiya ko kwanciyar hankali? Gara a ce an yi hakuri an jure tare da sadaukarwa na wani dan lokaci domin samun moriya mai dorewa.

Zage damtse wajen amfani da matakan kariya da shawarwarin masana, hanya ce mai sauki ta dakile wannan cuta. Yana da kyau jama'a su rika kula da wanke hannayensu da tsaftar muhalli da jiki da sanya marufin baki da hanci, da nisantar taro da sauransu, domin tabbatar kare kansu da sauran al'umma.

Ya kamata a gujewa yada jita–jita da labaran kanzon kurege, don kaucewa kara sanya fargaba da tsoro a zukatan jama'a. Maimakon haka, kamata ya yi a inganta wayar da kan jama'a, musamman masu karancin ilimi da mazauna yankunan karkara, dangane da hadarin cutar da kuma hanyoyin da za su kare kawunansu, domin har yanzu akwai wadanda ba su yadda da cutar ba, ko suke ganin ba za ta kama su ba saboda wasu dalilai, hakika wadannan rukunin mutane sun jahilci yanayin da duniya ke ciki, kuma wannan babban kalubale ne ga dukkan mutanen dake kewaye da su har ma da al'umma baki daya.

Rigakafi dai ya fi magani, kuma hanyar lafiya, an ce a bita da shekara. Abu ne mai muhimmanci daukacin al'umma su bada gudumuwa iya karfinsu, ba lallai gudunmuwa ta kudi ba, gudunmuwar kare kansu da kansu, domin ganin an gudu tare an tsira tare. (Faeza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China