Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
COVID-19 ba za ta hana tattalin arzikin Sin bunkasuwa ba
2020-04-29 17:15:12        cri

Tun bayan da kasar Sin ta yi nasarar dakile annobar COVID-19 a cikin kasar, yanzu ku san dukkan fannoni sun dawo bakin aikin a kasar, abin da ke nuna cewa, matakan da kasar ta dauka na yaki da cutar, sun yi matukar tasiri, har ma wasu kasashen duniya sun fara aiwatar da su a kasashensu.

Duk da cewa, annobar ta shafi tattalin arzikin duniya da sauran fannoni na rayuwa, wani masanin tattalin arzikin Amurka ya yi amanna cewa, managartan manufofin da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar sun tabbatar da saurin farfadowar tattalin arzikin kasar kuma akwai yiwuwar zai ci gaba da samun bunkasuwa yadda ya kamata.

Babban jami'in cibiyar nazarin tattalin arziki ta Milken Institute ta kasar Amurka Mr. William, ya ce kasar Sin ita ce kasa ta farko a duniya da ta kai ga dakile annobar covid-19, kuma ta dauki matakai a kan lokaci tare da aiwatar da manufofin bunkasa tattalin arzikinta, don haka, yana da kwarin gwiwa game da bunkasuwar tattalin arzikin Sin a watanni shida na karshen wannan shekarar. Himma aka ce ba ta ga Rago.

A yayin da tattalin arzikin Sin ke bunkasa, masanin ya ce, tattalin arzikin Amurka zai ja da baya a rubu'i na biyu da na uku na wannan shekarar, ya ce ya kamata Amurka ta yi koyi daga kasar Sin game da matakan farfado da tattalin arzikinta.

Amma abin takaici, shi ne rarrabuwar kawuna tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jahohin Amurka, ya sa sun kasa dakile annobar COVID-19 a kasar. Yadda kasar Sin ta farfado da sana'o'i daban daban bayan da ta dakile yaduwar cutar, ya kara shaida karfi da ingancin tattalin arzikin kasar wajen tinkarar matsaloli.

A baya-bayan ma, kasar Sin ta bayyana sake dagewa kananan sana'o'i dake cikin kasar haraji zuwa shekaru 4 masu zuwa, a wani mataki na kara kyautata hidimomin kudi ga wannan rukuni.

Tsarin sauwake haraji na baya-bayan nan da aka aiwatar, wanda aka tsara karewar sa a shekarar da ta gabata, a yanzu an kara shi zuwa ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2023, kamar yadda wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin ma'aikatar kudi da ta tattara harajin kasar suka fitar.

An dauki matakin ne domin tallafawa manufa, da karfafa gwiwar cibiyoyin hada hadar kudi, wajen samar da hidimomin kudi ga kananan sana'o'in. Tun a shekarar 2017 ne mahukuntan kasar suka ayyana janye harajin VAT ga hukumomi kudin kasar, bisa hada hadar da suka yi ta samar da basussuka masu ruwa ga kanana, da masu karamin jari, da ma sana'o'i da daidaikun mutane ke gudanarwa. Da ma sai da ruwan ciki ake jan na Rijiya.

Sanarwar ta kuma ce harajin VAT, wanda irin wadancan rukuni na masu sana'o'i suka riga suka biya, za a cire musu a watanni dake tafe, ko a mayar musu da kudaden su kai tsaye.

Masu fashin baki na cewa, matakan da mahukuntan kasar Sin suke dauka don bunkasa tattalin arzikin kasar duk da aikin dakile COVID-19 da ma taimakon da kasar ke baiwa sauran kasashen duniya a fannin fasahohi da kayayyakin aiki gami da tura jami'an lafiya, ya kara tabbatar da sahihancin dangantakar abokantar Sin da sauran kasashen duniya. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China