Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yada jita jita game da asalin cutar COVID-19 ba tare da sahihin dalili ba mummunan laifi ne
2020-04-30 17:19:14        cri

A wannan gaba da cutar numfashi ta COVID-19 ke ci gaba da mamayar sassan duniya, masu fadin albarkacin baki da dama sun dukufa wajen bayyana mahangar su game da asalin wannan cuta, inda wasu suka dage wajen yada jita jita, da karairayi a shafukan jaridu, da dandalin sada zumunta daban daban. Cikin irin wadannan ra'ayoyin mafi yamutsa hazo shi ne wanda wasu ke cewa wai a dakin gwaji aka kirkiri cutar, aka kuma yada ta domin cimma wasu manufofi.

Alal hakika ga duk wanda ke bibiyar masu baza irin wadannan jita jita, zai fahimci dalilai masu tarin yawa da suke ingiza su aikita wannan ta'asa. Cikin mafiya fitowa fili akwai wadanda ke yada jita jitar domin cimma manofofi na siyasa, ko kyamar salon gudanarwa, ko tsarin siyasar wani yanki. Akwai kuma masu son amfani da jita jitar wajen shawa wata kasa kashin kaji, ko kin jinin wata al'umma ko wasu addinai.

Ko shakka ba bu, kasar Sin ta kasance kasa wadda da yawa daga masu yada jita jita ke amfani da wadancan dalilai don aibatawa, ta hanyar nuna cewa ba ta bayyanawa duniya cikakkun bayanai game da halin da ta shi a baya ba, game da yaduwar wannan annoba ta COVID-19 a cikin gida, zarge zargen da ko alama ba su da tushe ko makama.

Idan mun dauki zargin da wasu ke yi cewa an kirkiri cutar COVID-19 ne a wani dakin gwajin kimiyya dake kasar Sin, za mu ga zargi ne da wadanda suka kirkire shi, ke fatan amfani da shi domin shafawa kasar Sin bakin fenti, duba da cewa masu yada shi ba su da wata shaida ta masana, sai dai kawai shaci fadi.

Idan ma aka yi duba ga kwayoyin cututtuka dangin Virus ciki hadda SARS-CoV-2, masu haifar da cuta ga mutane da dabbobi, dukkaninsu na da asali ne na halitta ta dabi'a, sabanin kirkira da wasu suke ganin an yi a dakin gwaji.

Bugu da kari, bisa al'ada yakan dauki masana dake bincike a fannin gano halayyar kwayoyin cututtuka tsawon lokaci kafin tabbatar da tushe, ko asalin wata kwayar cuta, amma abun mamaki a wannan lokaci wasu sun gama yanke hukunci, tare da dorawa kasar Sin laifin yaduwar COVID-19 ba tare da wani sahihin dalili ba.

A hannu guda kuma, tuni hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana cewa ba a kai ga tabbatar da asalin wannan cuta ba. Ko da ma batun cewa mai yiwuwa jemagu, ko dabbar pangolin ne suka yada COVID-19 zuwa mutane, hasashe ne kawai da har yanzu ba a kai ga tabbatar da shi a mahanga ta masana ba.

Sai dai fa duk da cewa masu yada jita jita game da asalin wannan annoba, ba sa gabatar da wasu dalilai sahihai na masana, duk da haka, matakin na su da dauke da wata mummunar guba, wadda ke haddasa kyamar kasar Sin, da kin jinin al'ummar ta. Hakan ya zama wani mummunan laifi da ya wajaba duniya ta yi tir da shi.

Kasancewar duniya na kara dunkulewa waje guda, kuma karin kasashe na dada fahimtar bukatar da ake da ita, ta hada karfi da karfi wajen yakar duk wata annoba da ta tunkari duniya, kamata ya yi dukkanin sassa su rungumi kaunar juna, da aiki tare, domin kawar da cutar COVID-19 daga duniya, kuma hakan ya zama darasi ga duniya, cewa "Duk abun da ya taba hanci ya kan sa idanu hawaye", wato dai dunkulewar duniya na kara tabbatar da muhimmancin kare makomar bil Adama ta bai daya.

Ko shakka babu duniyar bil Adama daya ce, kuma kare ta daga fitintunu, da kiyayya da kyamar wani sashe, ko wata al'umma, da ma bukatar hadin gwiwa domin cimma moriya tare, matakai ne da za su amfani daukacin bil Adama bai daya. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China