Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru a fadin duniya sun shaida bayanan da Sin ta gabatar da hadin gwiwarta da kasashen duniya kan cutar COVID-19
2020-04-07 12:07:27        cri
Kasar Sin ta fitar da wani jerin bayani kan yadda ta tunkari cutar COVID-19 a jiya Litinin, wanda ya zayyano muhimman bayanai da matakan da ta dauka wajen yaki da annobar a duniya.

Da suke tsokaci game da bayanan, kwararru daga kasashe daban-daban, sun shaida managartan matakan kariya da na dakile kwayar cutar Corona da Sin ta dauka. Sun kuma yi tsokaci kan kokarin kasar Sin na gabatar da matakanta ga sauran kasashen da kokarinta na inganta hadin kan kasa da kasa, inda suka ce wannan yunkuri ya taimaka wajen rage tasirin cutar.

Nina Ivanova, shugabar kungiyar kawance da huldar al'adu tsakanin kasashen waje da kasar Belarus, ta ce gwamnati da jama'ar Sin, sun gaggauata daukar ingantattun matakai bayan barkewar cutar, kana sun yi gagarumar sadaukarwa, wadda ta nuna karfi da hadin kan Sinawa.

A cewar Pierre Picquart, wani masanin harkokin kasar Sin dake Jami'ar Paris VIII, kasar Sin ta gabatar da ingantaccen misali da dabara ga sauran kasashen duniya, wanda ya tunatarwa duniya cewa, rayuwar bil adama na da makoma iri guda. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China