Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan talauci a Nijeriya ya kai kaso 40 cikin 100
2020-05-05 10:19:27        cri
Hukumar kididdiga ta Nijeriya ta ce yawan talauci a kasar ya kai kaso 40 cikin dari, wanda ya kai miliyan 82.9 na al'ummar kasar.

Hukumar ta ce yanayin talauci a birane ya tsaya ne kan kaso 18.04, yayin da ta yi kiyasin na yankunan karkara ya kai kaso 52.1 cikin 100.

Rahoton kan yanayin talauci da rashin daidaito a kasar na shekarar 2019, wanda hukumar ta fitar a jiya, ya ce ana auna matakin talauci a kasar ne da kudin da ake kashewa. A cewar hukumar, duk wani dan Nijeriya da abun da yake kashewa a shekara ya gaza kaiwa naira 137,430 (kimanin dala 381), to talaka ne.

Sai dai rahoton ya ware jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar, wadda ta shafe sama da shekaru 10 tana fama ayyukan ta'addanci na kungiyar BH.

A matsayinta na wadda ta fi kowacce kasa samar da mai a nahiyar Afrika, kudin shiga da farashin musayar kudaden ketare a Nijeriya, sun dogara ne sosai kan sayar da man fetur ga kasashen ketare.

Masu nazari a kasar, sun yi gargadin cewa, bisa la'akari da faduwar farashin man fetur, wanda ya hadu da annobar COVID-19, akwai yiwuwar fuskantar faduwar tattalin arzikin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China