Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu dauke da COVID-19 a Najeriya ya kai mutum 2,558
2020-05-04 20:57:33        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya ko NCDC a takaice, ta ce karin mutane 170 sun harbu da cutar numfashi ta COVID-19, wanda hakan ya daga adadin masu dauke da cutar a Najeriya zuwa mutum 2,558.

Cikin sanarwar da ta fitar, NCDC ta ce karin mutane 2 sun rasu a daren ranar Lahadi, wanda hakan ya kara jimillar wadanda cutar ta hallaka zuwa mutum 87.

A daya bangaren kuma, cibiyar ta ce kawo yanzu, adadin wadanda ke fama da cutar ya kai mutum 2,017, sai kuma mutane 400 da aka yiwa magani suka warke, aka kuma sallame su. Har ila yau cibiyar ta ce ta fara aiwatar da sabbin dabarun gwaji, da shawo kan cutar, bayan da aka tabbatar da fara yaduwarta a tsakanin al'ummun kasar.

Daya daga dabarun da ake amfani da su a cewar NCDC, shi ne gwada marasa lafiya dake fama da tari, ko zazzabi, ko wadanda suka yi fama da zazzabi a baya, musamman cikin makwanni 2 da suka gabata, masu kuma dauke da daya, ko sama da daya, cikin manyan alamun harbuwa da wannan cuta ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China