Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF ya yanke kudurin ba Nijeriya rance dallar Amurka biliyan 3.4
2020-04-30 11:56:28        cri
Bisa labarin da aka samu, a jiya Laraba, Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yanke shawarar samar wa Nijeriya rancen kudi na gaggawa na dallar Amurka biliyan 3.4, domin taimakawa kasar wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Rancen ya kasance mafi yawa da IMF ya samar ga kasar Afirka wajen dalike yaduwar wata cuta, kuma bisa shirin da aka tsara, Nijeriya za ta biya bashin cikin shekaru biyar masu zuwa. Ban da haka kuma, a jiya Laraba, majalisar dattawan kasar ta amince da bukatar da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar na neman sabon rancen Naira biliyan 850 daga kasuwannin hada-hadar kudi. Sa'an nan kuma, gwamnatin kasar Jamus ta sanar soke bashin da take bin Nijeriya na Euro miliyan 22.4, yayin da ta samarwa kasar taimakon jin kai na Euro miliyan 5.5, domin taimakawa jihohinta na yankin arewa maso gabas, kamar jihar Borno, jihar Yobe da kuma jihar Adamawa da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China