Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu cutar COVID-19 a Nijeriya ya zarce 2,000
2020-05-02 15:57:11        cri
An tabbatar da samun sabbin mutane 238 da suka kamu da cutar COVID-19 da yammacin jiya Juma'a a Nijeriya, wanda ya kawo jimilar adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar zuwa 2,170, ciki har da 68 da suka mutu da kuma 351 da suka warke.

Adadin na jiya, shi ne mafi yawa da aka samu cikin rana guda a kasar tun bayan bullar cutar.

A cewar hukumar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta kasar NCDC, an samu sabbin wadanda suka kamu da cutar ne a jihohi 21 na kasar da birnin tarayya Abuja.

Tun bayan bullar annobar a kasar a ranar 27 ga watan Fabreru, kasar ta dauki ingantattun matakai da nufin dakile yaduwar cutar a kasar mafi yawan al'umma a Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China