2020-04-27 13:43:48 cri |
William, babban jami'in cibiyar nazarin tattalin arziki ta Milken Institute ta kasar Amurka, yace kasar Sin itace kasa ta farko a duniya da ta kai ga dakile annobar covid-19, kuma ta dauki matakai akan lokaci kana ta aiwatar da manufofin bunkasa tattalin arzikinta, ya kara da cewa, yana da kwarin gwiwa game da bunkasuwar tattalin arzikin Sin a watanni shida na karshen wannan shekarar.
William ya ce, a ganin masana tattalin arzikin Amurka, tattalin arzikin Amurka zai ja da baya a rubu'i na biyu da na uku na wannan shekarar, yace ya kamata Amurka ta yi koyi daga kasar Sin game da matakan farfado da tattalin arzikinta.
David uribe, shehun malami a jami'ar jahar California, yayi imanin cewa, rashin samun hadin kai tsakanin gwamnatin tarayyar da kananan hukumoimn jahohin Amurka ya sa sun rasa samun damar dakile annobar COVID-19 a kasar. Yadda kasar Sin ta farfado da sana'o'i daban daban bayan da ta dakile yaduwar cutar, ya kuma shaida karfi da ingancin tattalin arzikin kasar wajen tinkarar matsaloli.(Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China