Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jirgin kamfanin Boeing ya yi jigilar takunkumin rufe baki da hanci miliyan 1.5 daga Sin zuwa Amurka
2020-04-27 10:52:53        cri
A jiya Lahadi ne jirgin dakon kaya na kamfanin Boeing ya kammala jigilar kayayyakin bada kariyar lafiya na takunkumin rufe baki da hanci har miliyan 1.5 daga Sin zuwa Amurka.

Wata sanarwa da aka fitar ta bayyana cewa, kamfanin ya yi jigilar kayayyakin ne domin amfanin jami'an lafiya dake aiki a cibiyar Prisma dake kudancin Carolina, da hadin gwiwar hukumar Prisma Health, da kafanonin Atlas Air da Discommon.

Discommon, ne ya yi odar kayan daga wani kamfanin kasar Sin, ya kuma bukaci kamfanin jiragen sama na Boeing da ya yi jigilar su zuwa hukumar Prisma Health, wadda ita ce babbar hukumar kula da lafiya ta kudancin Carolina.

Kamfanin Boeing ya ba da tallafin hidimar sufuri, wadda kamfanin Atlas Air ya aiwatar a madadin sa. A nan gaba kuma, ana sa ran jiragen kamfanin na Boeing da na ecoDemonstrator, za su kara yin makamancin wannan aiki.

A ranar 18 ga watan Afirilun nan ma dai kamfanin Boeing, ya kammala zangon farko na jigilar kayayyakin kandagarkin cutar COVID-19, ta amfani da samfurin jirgin sa mai lamba 737-700, wanda ya yi dakon wasu kayan zuwa Amurka. (SAMINU)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China