Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Filin jirgin saman kasa da kasa na Tripoli zai dawo bakin aiki a ranar 12 ga watan Disamba
2019-12-02 10:58:01        cri

Ma'aikatar sufurin gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD ta sanar a jiya Lahadi cewa filin jirgin saman kasa da kasa na Mitiga dake babban birnin kasar Libya Tripoli zai dawo bakin aiki a ranar 12 ga wannan wata na Disamba.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ya nuna cewa, bayan kammala wani taron tattaunawa da aka gudanar game da ci gaban da aka samu a baya-bayan nan, an yanke shawarar sake bude filin jirgin saman daga ranar 12 ga wannan wata.

An rufe filin jirgin saman kasa da kasa na Mitiga ne a watan Satumba bayan barnar da aka samu sakamakon jefa wasu abubuwan fashewa, tun daga wancan lokacin aka karkatar da dukkan tashi da saukar jirage daga filin jirgin saman zuwa filin jirgin saman kasa da kasa na birnin Misurata, mai tazarar kilomita 200 daga gabashin Tripoli.

Sojoji masu sansani a gabashin kasar, karkashin jagorancin Khalifa Haftar, sun sha kaddamar da hare-haren soji a yankunan birnin Tripoli da kewayensa, da nufin kwace ikon birnin da kifar da gwamnatin mai samun goyon bayan MDD.

Dubban mutane aka hallaka da kuma jikkata wasu da dama a fadan da ake gwabzawa, sannan mutane sama da 120,000 ne fadan ya yi sanadiyyar raba su da gidajensu.

Duk da irin gargadin da MDD ke yi, filayen jirgin saman na Mitiga da Misurata suna ci gaba da fuskantar yunkurin kai hare-hare tun bayan barkewar tashin hankalin masu dauke da makamai.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China