Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi kira a tafiyar da takunkuman Libya yadda ya kamata
2019-11-19 10:56:19        cri
Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira da a tafiyar da takunkuman da aka kakabawa Libya yadda ya kamata, domin ba a sanya su domin son zuciya ba, sai don samar da maslaha ga rikicin kasar.

Yayin taron kwamitin Sulhu na majalisar a jiya, Wu Haitao, ya ce duba da yanayin da ake ciki yanzu, ya kamata a tabbatar da aiwatar da takunkuman makamai da majalisar ta sanyawa Libyan yadda ya kamata, sannan a kaucewa munanan tasirin da za su haifar ga fararen hula a sauran yankunan kasar da sauran kasashe.

Ya bayyana cewa, Libya ta bayyana damuwa kan ci gaba da durkushewar kadarorinta da aka hana amfani da su da sauran asara masu alaka da takunkuman, yana mai cewa ya kamata kwamitin dake kula da aiwatar da takunkumin ya gaggauta aikinsa na samo hanyoyin da suka dace na tunkarar halaltattun korafin Libya.

Har ila yau, wakilin na kasar Sin, ya bukaci kwamitin da tawagar kwararunsa dake kula da takunkuman da Sakatariyar MDD, su kiyaye manufofin takunkuman da kuma tabbatar da suna ayyukan da suka dace ba tare da bangaranci ba.

Tun daga shekarar 2011 Libya ke ta fama da rikicin siyasa da rashin tsaro, bayan hambarar da mulkin tsohon shugaban kasar, Muammar Gaddafi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China