Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Senegal ta kaddamar da shirin tallafin abinci ga gidaje miliyan 1 da cutar COVID-19 ta shafa
2020-04-29 11:48:07        cri

Gwamnatin Senegal, ta kaddamar da shirin rabon tallafin abinci, domin taimakawa gidaje miliyan 1 da cutar COVID-19 ta shafa.

An yi bikin kaddamar da shirin ne jiya, a gaban wasu daga cikin wadanda suka ci gajiya da jami'an hukumomin da zababbun jami'ai, a birnin Pikine, dake gabas da birnin Dakar.

Ministan kula da harkokin raya al'umma da daidaito tsakanin yankuna, Mansour Faye, ya ce bikin ya kaddamar da shirin a hukumance a fadin kasar.

Mansour Faye, ya ce rabon kayayyakin abinci a fadin kasar babban aiki ne dake bukatar dukkan al'umma da kungiyoyinsu da ma 'yan siyasa.

Ya kuma yi bayanin cewa, za a raba tallafin ne ga gidaje miliyan 1, wanda zai kunshi 'yan kasar kimanin miliyan 8 zuwa 10. Ya ce kowanne gida zai samu shinkafa kilo 100 da suga kilo 10 da mai lita 10 da sabulai 18, wadanda darajarsu ta kai kimanin kudin kasar Francs CFA 66,000, kwatankwacin dalar Amurka 109. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China