Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Motoci 30 sun kone sanadiyyar wata gobara a Nijeriya
2020-04-29 12:23:59        cri
Motoci a kalla 30 sun kone sanadiyyar wata gobara da ta tashi a wani gidan mai dake yankin Ogba na jihar Lagos, cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Nijeriya.

Darakta janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Olufemi Oke Osanyintolu, ya ce ba a samu asarar rai sanadiyyar iftila'in ba.

An ga yadda hayaki da wuta suka turnuke sararin samaniya a yawancin sassan birnin lagos, bayan tanka mai dauke da man diesel lita 33,000 ya kama da wuta a lokacin da yake sauke man da yake dauke da shi.

A cewar Olufemi Oke-Osanyintolu, an yi nasarar kashe wutar baki daya tare da shawo kan yanayin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China