Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Nijeriya ya sanar da sassauta matakan kulle
2020-04-28 13:51:33        cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sanar da cewa, yayin da kasar ke ci gaba da yaki da COVID-19, za a sassauta matakan kulle daki-daki a Abuja, babban birnin kasar da jihohin Lagos da Ogun, daga ranar 4 ga watan Mayu.

Cikin jawabinsa da aka watsa kai tsaye a daren jiya, Muhammadu Buhari ya ce cikin makonni 4 da suka gabata, galibin sassan kasar sun kasance karkashin dokar kulle daga gwamnatin tarayya ko ta jihohi, matakin da ya taimaka wajen rage yaduwar cutar a kasar. Sai dai, ya ce matakan sun yi mummunan tasiri akan harkokin tattalin arziki.

Muhammadu Buhari ya kuma sanar da sabbin matakan da za su maye gurbin na kulle a fadin kasar, ciki har da dokar hana fita daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safiya, da haramta duk wasu tafiye-tafiye da basu da muhimmanci tsakanin jihohin kasar, da tilasta sanya marufin hanci da baki a wuraren jama'a, da kuma sanya ido kan sufurin kayayyakin abinci tsakanin jihohi.

Ya ce baya ga matakan, za a kuma a matse kaimi wajen yin gwaji da bibiyar wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu da cutar, tare kuma da dawo da wasu harkokin kasuwanci da na tattalin arziki a wasu bangarori.

Sai dai, ya ce har yanzu dokar hana taron jama'a da na addini bata sauya ba, yana mai cewa za a ci gaba da dokar kulle a birnin Abuja da jihohin Ogun da Lagos, har zuwa lokacin da za a fara aiwatar da sabbin matakan a ranar Litinin mai zuwa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China