Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Ghana ya kai 636
2020-04-15 10:41:05        cri

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar Ghana ya karu zuwa 636, bayan an tabbatar sabbin mutane 70 sun kamu da cutar a jiya.

A cewar hukumar kula da lafiya ta kasar (GHS), cikin dukkan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, kaso 70 ba su yi tafiya ba, tana mai cewa kawo yanzu an yi wa mutane 44,421 gwaji.

Hukumar ta GHS ta alakanta karuwar adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar da tsauraran matakan da aka dauka, ciki har da matse kaimi wajen bibiyar wadanda suka yi mu'amala da masu cutar da kuma gudanar da gwaji.

Baya ga haka, mutane 8 sun mutu sanadiyyar cutar, yayin da aka sallami wasu 17 bayan sun warke, a kasar dake yammacin Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China