Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 40 da aka yi gwaji a Ghana ba sa dauke da cutar COVID-19
2020-03-05 20:29:24        cri
Ministan lafiya na kasar Ghana Kwaku Agyeman-Manu ya bayyana cewa, sakamakon gwajin da aka yiwa kimanin mutane 40 da ake zaton suna dauke da cutar COVID-19, ya nuna ba sa dauke da cutar.

Ministan ya bayyana cewa, kasarsa ta tsaurara matakanta na kandagarki, kamar yadda MDD ta ba da shawarwari ga kasashen mambobin majalisar, kan su shirya da ma hana kara yaduwar cutar.

Mutuwar dan kasar ta Ghana na baya-bayan da ya dawo daga kasar Jamus, ya haifar da jita-jita cewa, dan kasar ta Ghana ta kamu da cutar COVID-19, amma daga bisani, sakamakon gwajin da aka yi ya nuna cewa, ba cutar ce ta kashe shi ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China