Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Ghana ya kai 204
2020-04-03 10:24:51        cri
Hukumar lafiyar kasar Ghana ta sanar a jiya Alhamis cewa, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar ya karu zuwa 204.

Dukkan sabbin mutanen da suka kamu da cutar a Accra ne, babban birnin kasar.

Hudu daga cikin mutanen ba su da tarihin zuwa wasu kasashe, sannan mutane hudu daga cikinsu sun yi mu'amala da masu dauke da cutar, kana mutum daga cikin adadin ya shiga kasar Ghana ne daga jamhuriyar Benin a kwanaki 14 da suka gabata.

Kawo yanzu kasar ta yammacin Afrika ta samu mutuwar mutane 5 kana wasu mutane 3 sun warke daga cutar ta COVID-19, sannan akwai mutane 49 da yanayin lafiyar yake kara kyautata a inda ake kula da su. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China